Femi Hamzat

Femi Hamzat
Deputy Governor of Lagos State (en) Fassara

29 Mayu 2019 -
Oluranti Adebule
Rayuwa
Haihuwa Lagos, 19 Satumba 1964 (59 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Yarbanci
Karatu
Makaranta Jami'ar Ibadan
Harsuna Turanci
Yarbanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da injiniya
Imani
Jam'iyar siyasa All Progressives Congress

Kadri Obafemi Hamzat (An haife shi 19 ga watan Satumban 1964) ɗan siyasar Najeriya ne wanda ya zama mataimakin gwamnan jihar Legas tun 2019.[1]

An haife shi a Legas a cikin dangin Late Oba Mufutau Olatunji Hamzat da Late Alhaja Kehinde Hamzat daga Iga Egbe dake Jihar Legas. Mahaifinsa, Marigayi Oba Mufutau Olatunji Hamzat ya taɓa zama ɗan majalisar dokokin jihar Legas kuma kwamishinan sufuri a jihar daga 1979 zuwa 1983 kafin ya zama mataimakin shugaba (South West) na Alliance for Democracy (AD) a lokacin).[2] Ya zama shugaban majalisar dattawan Legas ta yamma na jam'iyyar Action Congress kuma ya zama sarki ta hanyar zuriyarsa ta sarautar uwa.

  1. https://thenationonlineng.net/ampion-microsoft-support-200-smes/
  2. https://www.thisdaylive.com/index.php/2019/09/22/obafemi-hamzat-at-54/

© MMXXIII Rich X Search. We shall prevail. All rights reserved. Rich X Search